A jiya Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan wani jigo a jam’iyyar APC kuma dan takarar gwamna a jihar Jigawa, wato Farouk Adamu Aliyu dake jihar Kano.
‘Yan bindigar wadanda aka ce sun kai kusan 10, sun kai harin ne a gidan sa dake Babura Road a unguwar Nasarawa dake cikin birnin Kano da misalin karfe biyu na dare.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa shine kakakin rundunar Ƴan sandan Kano, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce duk da ‘yan bindigar sun gaza shiga gidan, amma sai da suka nemi Jikkata masu gadin gidan.
A wasu rahotanni da jaridar Dimokuraɗiyya ta samu, sun bayyana cewa daya daga cikin masu gadin gidan ya samu rauni bayan da suka sare shi da adda yayin da sauran kuma aka daure su.
An ce ihun da mai gadin da ya ji rauni yayi tayi ne ya ja hankalin makwabta suka kira ‘yan sanda, kuma an ce jigon na APC din ba ya cikin gidan a lokacin da aka kai harin.
SP Haruna Kiyawa, ya ce da yan sanda suka samu labarin ta kiran da akai musu ta lambar su ta gaggawa, ‘yan sandan sun kai daukin nan take.
”Kwamishinan ‘yan sandan CP Samaila S. Dikko ya tada tare da umurtar tawagar ‘Operation Puff Adder’ zuwa wurin.”
“Ganin ‘yan sandan ya sanya ‘yan fashi da makamin guduwa. Sai dai an fara bincike domin kamo duk wadanda ke da hannu a ciki tare da gurfanar da su a gaban kuliya,” inji Kiyawa.
A karshe ya tabbatar da cewa basu kai ga gano bata garin ba amma suna nan suna ci gaba da bincike da nufin zakulo su tare da gabatar da su gaban Shari’a.