A daren jumma’a ne yan ta’adda suka kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, a kauyen Bafarawa dake jihar Sakkwato. Bayani ya nuna cewa, tshon gwamnan baya a cikin gidan a lokacin da ka akai harin, amma yan bindigan sun samu nasarar kashe mai gadin gidan mai suna, Abdullahi Jijji sun kuma yi awon gaba da wani yaro mai suna Abdulrasheed Sa’idu. A wata sanarwa da Darakta Janar na gidauniya Attahiru Bafarawa, ya ce, yan bindigan sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi suka kuma yi barazanar kashe dukkan mutanen kayukan Bafarawa da Kamarawa. Dukkan kauyukan na karkashin karamar hukumar Isa ne ta jihar. “Wannna shi ne karo na farko da aka kawo irin wannan hari a Bafarawa amma mutanen kauyen Kamarawa dake kusa damu sun sha samun wadannan hare haren abin daya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a lokuttan baya. ”’A ranar Alhamin da ya gabata ne, tsohon Gwamna Bafarawa ya zanta da ‘yan jarida inda ya bayyana shirinsa na shiriya babban taro a kan matsalolin tsaron da ake fama dasu, taron zai hada manyan Arewa, gidauniyar Attahiru Bafarawa za ta dauki nayin shirin da nufin samar da hanyoyin kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar, ya zuwa yanzu rundunar yan sandan jihar basu yi tsokaci a kan lamarin ba.