Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari tare da kashe mutane biyu a kauyen Ungwan Taila, da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Sojojin Operation Safe Haven ne suka ruwaito wannan labarin.
Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Mista Samuel Aruwan ne wanda ya tabbatar da hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, sojojin sun isa kauyen ne bayan sun gano cewa, maharan sun kashe mazauna garin guda biyu.
A cewar sanarwar, Gwamna Nasir el-Rufai ya bayyana matukar damuwar sa kan harin da yayi sanadiyar asarar rayuka a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar PDP ta Lashe Zaben Karamar Hukumar Zangon Kataf na Kaduna
A karshe Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan mamatan, sannan ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan su.