Akalla mutane biyu ne aka kwantar a asibiti bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu.
Shugaban Hukumar INEC, a sashen Watsa Labarai da Ilimantar da masu Zabe, Festus Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Alhamis.
Ya ce maharan sun lalata na’urar tantance masu kada kuri’a guda biyu a yayin harin
Sanarwar ta bayyana cewa an kai wa jami’an hari ne a yayin da suke ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a (CVR) a wata makarantar firamare da ke Umuopu da ke Umuozzi Ward 19 a jihar Enugu.
Ya ce, “’yan bindigar sun yi ta harbe-harbe ba kakkautawa don tarwatsa masu rajista da jami’an rajista. A rikicin da ya biyo baya, daya daga cikin ma’aikatanmu ya samu raunuka kuma yana karbar magani a asibiti,” in ji sanarwar.
“An yi asarar injunan rajistar masu kada kuri’a guda biyu da kayayyakin ma’aikata kamar wayoyin hannu.
“Saboda haka, an dakatar da rajistar masu kada kuri’a a gundumar a Igboeze North.”
A cewar Okoye, hukumar ta kai rahoton lamarin ga hukumomin ‘yan sanda a jihar Enugu domin fara bincike.
A wani labarin kuma na daban
‘Yan sanda sun bankado wani gidan samar da jarirai a Delta
Rundunar ‘yan sanda a jihar Delta ta tabbatar da gano wani gidan Samar da jarirai a unguwar Okpanam da ke karamar hukumar Oshimili ta Arewa a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Bright Edafe, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a garin Asaba, inda ya ce jami’an ‘yan sanda daga hukumar bincike ta jihar (SID) da suka far wa wurin, sun ceto wasu mata masu juna biyu guda uku.
“A bisa bayanai, a ranar 10 ga Yuli, 2022, da misalin karfe 7:30 na yamma, jami’an hukumar bincike na jihar sun kai farmaki a wata masana’anta da ke unguwar Okpanam, karamar hukumar Oshimili ta Arewa.
“Jami’an sun ceto mata masu juna biyu guda uku da wasu mutane biyu da ake zargi; An kama Promise Ejogu da Aruna Sulieman.
“Bayanan da ‘yan sanda suka tattara sun nuna cewa daya daga cikin wadanda ake zargin Promise Ejogu, dan uwa ne ga shugaban wata kungiyar .
Edafe ya ce “Kungiyar ta ci gaba da rike matan kuma tana sanya su cikin ayyukan jima’i don daukar ciki,” in ji Edafe.
Kakakin ‘yan sandan ya ce a halin yanzu wadanda ake zargin suna tsare yayin da ake kokarin cafke sauran ‘yan kungiyar. (NAN)