Wasu ‘yan bindiga a ranar Alhamis da yamma sun yi artabu da sojoji a wani shingen bincike da ke Zuma Rock Madalla, kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Har yanzu ba a bayyana ko an samu asarar rayuka ba.
A cewar majiyoyi da dama, lamarin ya haifar da kulle kan babbar.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/za-mu-sau%c6%99a%c6%99a-rayuwar-al%c6%99alai-a-najeriya-shugaba-buhari/
Wani ganau ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa harin ya fara ne da misalin karfe 8 na dare.
Hukumomin ‘yan sanda da na soji ba su kai ga kai dauki ba kan lamarin.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wannan hari na baya bayan nan da aka kai kan wani sansanin soji na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani bangare na masu gadin fadar shugaban kasa, inda suka kashe sojoji akalla uku.