Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani kamfanin gine-gine a garin Owo na jihar Ondo.
An kuma ruwaito cewa, an yi harbe-harbe a kamfanin sarrafa kayayyakin gine-gine na Craneburg, dake garin na Owo a yammacin jiya Laraba.
A wani sako da rundunar ‘yan sandan kasar nan ta wallafa a shafinta na twitter ta tabbatar da cewa an jikkata wasu mutane yayin harin.
Rundunar ta ce, an yi harbe-harbe a kamfanin na Craneburg, dake garin Owo a daren jiya Laraba.
Rahotanni sun bayyanacewa, a halin yanzu jami’an ‘yan sanda na jibge a wurin da lamarin ya afku, inda kuma a kai wadanda harin ya rutsa da su asibiti domin samun kulawar likitoci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Shirin Fitar Da ‘Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Kangin Talauci
Babban jami’in tsaro na kamfanin, Tubsun Aladeselu ya tabbatarwa da gidan Talabijin na Channels cewa biyu daga cikin ma’aikatan da suka samu raunuka harbin bindiga a yayin harin suna samun kulawa a wani asibiti da ke kusa da inda lamarin ya afku.
Ya ce maharan wadanda adadinsu ya kai 2, sun zo ne a cikin wata motar safa, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
Ya kara da cewa, ‘yan ta’addan sun kuma yi amfani da wani abu mai fashewa.
Sai dai ruwaito cewa maharan sun isa wurin ne da misalin karfe 9 na dare yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya, kuma yawancin ma’aikatan na cikin Kamfanin.
Rayhaan Radio ta ruwaito cewa, kimanin watanni biyu da suka gabata, an yi garkuwa da wani injiniya dan kasar waje a kamfanin, sannan aka harbe wani sojan da ke gadinsa a wani wuri dake garin Owo.
Kazalika Idan dai za a iya tunawa, a watan da ya gabata, ‘yan bindiga sun kashe wasu masu ibada a wata coci a garin Owo.
A yayin harin Cocin, ‘Yan bindigar sun shiga cocin St Francis Catholic da ke garin Owo inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi a lokacin da suke tsaka da gudanar da ibada.
A halin da ake ciki, Gwamnatin Tarayya ta zargi kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP da kai harin cocin Owo, amma Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce an yi gaggawar yin wannan zargi.
A baya dai, Jihar Ondo ta sha fuskantar tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya a shekarun baya-bayan nan.