Da yammacin ranar Alhamis din data gabata ne Yan bindiga a jihar Zamfara, suka kai hari garin Shinkafi, ciki har da ofisoshin yan sanda guda biyu, inda sukai ta harbe -harbe kan Mai uwa da wabi, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa, maharan sun yi awon gaba da makamai daga ofisoshin yan sandan da suka yi wa kawanya.
Sai dai haryanzu Babu Cikakkun bayanai kan abin da ya faru ya yin hada wannan rahoton, saboda garin Shinkafi kamar sauran garuruwa ya ke a jihar Zamafara, saboda rufe hanyoyin sadarwa da Gwamnatin jihar tayi tun a farkon wannan wata da muke ciki.
Amma wani mazaunin garin wanda ya yi magana daga jihar Sokoto, ya tabbatar da rahoton kai harin, ta kafofin sada zumunta a safiyar jiya Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kogi ta Umarci al’umar wasu yankuna da su bar Gidajen su
Ya ce yan bindigar sun isa garin lokacin da mazauna garin ke sallar magriba, kuma sun kwashe sama da awa guda yayin da suka farmaki garin .
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, harin ya biyo bayan wasikar barazana da aka aika wa al’ummar yankin a farkon makon nan, inda shugabannin Yan bindiga biyu da ke kusa da yankin, Kachalla Turji da Halilu Sububu, suka sanar da hadin gwiwar kai farmaki kan Shinkafi da kewayenta.
Shinkafi ita ce babban birni na karshe a kan hanyar da ke hada Zamfara da Jihar Sokoto mai makwabtaka da juna.
Kazalika Daily Trust ta ce, duk yunkurin ta na zantawa da Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Zamfara ya citira, saboda rufe hanyoyin sadarwar jihar da aka yi, yayin da kakakin rundunar yan sandan Nigeria, CP Frank Mba, ya ce ba shi da labari kan Kai wannan harin.