An kashe Kenneth Ibe dalibi dake karatun digiri a jami’ar Jihar Imo na garin Owerri, wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi.
Dalibin dan asalin karamar hukumar Isiala Mbano na jihar Imo ne, yayin da wadanda suka sace shi su kashe shi a ranar Juma’ar data gabata, sannan suka jefar da gawar sa a kan hanya.
Abokansa sun yi ta Wallafa sakonnin fatan Alheri ga Yan’uwasa a kafar sada zumunta na Facebook don yi masa ta’aziyya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Muna son Jami’iyyar APC tayi shekaru 50 tana mulki — inji Ali Modu Sheriff
Chidiebube Okeoma, daya daga cikin danginsa, ya bayyana kisan a matsayin “abin takaici”
A cikin sakon, Okeoma ya ce, “Kisan dan uwanmu daga karamar hukumar Isiala Mbano wato Kenneth Ibe, dalibin dake aji 3 na jami’ar jihar Imo, abin takaici ne” inji shi.
Har yanzu rundunar yan sanda ba ta ce komai ba kan lamarin, yayin da kakakin rundunar yan sandan jihar CSP Mike Abattam ba’asami damar hi ta bakin shi ba.
A Wani Labarin Kuma
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a daren jiya Asabar sun kai hari kan wani gidan gona a kauyen Ahun dake yankin Oro Ago na karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.
An kashe wata budurwa, mai suna Rukayat, sanadiyar harin.
Lamarin ya haifar da mummunan tashin hankali a tsakanin al’umma yankin, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu mutane biyu sun samu raunukan harbin bindiga sanadiyar harin.
Sai dai Ba’a tantance halin da wadanda suka ji raunikan ke ciki ba, harkawo hada wannan rahoton.
Mai magana da yawun rundunar tsaro ta farin kaya da kare kaddarorin Gwamnatin NSCDC reshen jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, jami’an tsaro sun dura yankin da kewayen domin dakile wasu hare -hare a nan gaba
“Lamarin ya faru da misalin karfe 8:00 na daren jiya Asabar. Yayin da Yan bindigar masu yawan gaske, suka afka yankin kuma suka fara harbe-harbe ba zato ba tsammani.
“An kashe wata yarinya, wacce harsashi ya same ta, yayin da wasu biyu da suka samu raunuka aka kai su asibiti don yi musu magani,” inji shi.
Ya kara da cewa, ana ci gaba da bincike kuma rundunar na aiki tare da shugabannin al’umma don gano musabbabin Kai hari.
Comments 1