Mutane hudu ne suka mutu sakamakon wani hari da wasu mmutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai a kauyen Fapo da ke karamar hukumar Lapai a jihar Neja.
An kuma ruwaito cewa mutane 8 sun samu munanan raunuka a daidai lokacin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da 15 a harin da aka kai da sanyin safiyar ranar Litinin a kauyen.
KARANATA WANNAN LABARIN: 2023: Masu Neman Takara A APC Kaduna Sun Janye Kararrakin Da Suka Shigar Kotu
DAILY POST ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun mamaye kauyen da yawa akan babura, inda suka rika hari ba kakkautawa tare da haifar da fargaba yayin da suke gudanar da aikinsu na ta’addanci.
Danlami Idris wani shaidan gani da ido ya bayyana kaduwarsa a kan yadda ‘yan bindigar suka far wa kauyen suna harbe-harbe kai tsaye, lamarin da ya haifar da firgici tare da kashe mutane hudu.
Ya bukaci gwamnatin jihar da jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A cewarsa, “Muna kira ga gwamnatin jihar da jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen ganin an kaucewa hare-haren da za su haifar da barna a cikin al’ummar jihar nan gaba”.
A halin da ake ciki, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO DSP Wasiu Abiodun, har yanzu bai amsa kiran da aka yi masa ba kan harin.
A WANI LABARIN KUMA: Rundunar Yan sandan Jihar Benue Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutum Uku
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue a ranar Litinin ta tabbatar da kashe mutane uku a wani hari da aka kai kauyen Tse Ngban da ke unguwar Nyiev a karamar hukumar Guma a jihar Benue.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, SP. Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an aika gawar wadanda suka mutun zuwa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.