By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani jami’in hukumar DSS a lokacin da suka kai hari a garin Abaji dake karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Asabar.
An kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kashe wani dan banga a lokacin da lamarin ya faru cikin dare.
Ance ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar yankin da ba’a bayyana adadin su ba inda suka kai hari a ofishin DSS dake yankin.
A yayin musayar harbe-harbe da jami’an DSS, ‘yan bindigar sun yi nasarar yin garkuwa da wani jami’in hukumar ta DSS.
Sai dai har yanzu Wakilanmu bai iya samun tabbacin ko ‘yan kungiyar ta’addan sun nemi kudin fansa ga jami’in da aka sace ba.
Mai magana da yawun ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, tace ba ta da labarin faruwar lamarin, ta kuma mika bincike ga hukumar ta DSS.
Sai dai kuma da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunanya, ya musanta zargin, ya kuma ce babu wani jami’in su da aka sace.
Afunanya a wata sanarwa daya fitar ta kafar sadarwar Whatsapp yace, “Babu wani jami’in DSS da aka sace a Abaji ko kuma a cikin birnin tarayya FCT.”