Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe direbobin manyan motoci biyu na kasa Moroko tare da jikkata wani a unguwar Didieni, kilomita 300 daga Bamako babban birnin Mali, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Morocco MAP a ranar Lahadi.
Direbobin manyan motocin sun nufi Bamako dauke da kayayyaki kafin wasu gungun mutane dauke da makamai da suka boye a bayan bishiyoyi a gefen hanya suka far musu.
Ya ce, ‘yan bindigar sun lullube kawunansu, sanye da rigunan kariya daga harsashi kuma suna da na’urorin sadarwa mara waya.
Ya kara da cewa sun bar wurin ba tare da sun sace komai daga wadanda abin ya shafa ba.
An tura direban da ya jikkata zuwa asibitin yankin don samun kulawar da ta dace, in ji shi.
Kasar Morocco tana da huldar kasuwanci mai karfi da kasashen yammacin Afirka.
Da yawa daga cikin manyan motocin Moroko na tsallaka hanyar Sahel ta bi ta Mauritania da Mali a kowace rana don jigilar kayayyaki tsakanin ƙasashe daban -daban na yankin.