Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane da dama a wasu sabbin hare-hare da suka Kai kan wasu kauyuka biyu na Yagbak da Ungwan Ruhugo da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
An bayyana hakan ne ta wata sanarwa da kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a jiya.
Sanarwar ta kara da cewa hukumomin soji da na ‘yan sanda sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna harin da aka kai a wurare biyu.
A cewar sanarwar, an kashe wasu mutane yayin da wasu da dama suka samu raunuka, sannan an kona wasu gidaje a wuraren biyu.
Ya kara da cewa: “Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, domin ana jiran cikakkun bayanai daga Jami’an sojoji, ‘yan sanda da kuma naDSS a wuraren biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 3 sun Mutu yayin da Gobara ta tashi a wata kasuwa dake Abuja
“Za a ba da ƙarin bayani ga jama’a da zarar an tabbatar da waɗannan munanan harin.”.
Kazalika Sanarwar ta ce, “Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da hare-haren, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda abin ya shafa, ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta gudanar da ta ziyarci yankin cikin gaggawa tare da samar da kayan agaji ga al’ummomin da abun ya shafa.”