Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani Ladani a lokacin da yake kiran sallar Asubahi a unguwar Magazu da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilin Jaridar Daily trust cewa, Ladanin na cikin masallacin da ke kusa da gidansa ne, sai ‘yan bindigar suka kai masa hari suka harbe shi.
Magazu mai tazarar kilomita 40 kudu da Gusau, babban birnin jihar, a kan hanyar Gusau zuwa Funtua, ya fusata masu laifin bayan an gano gawar abokin aikinsu da aka kashe a kusa da unguwar kwanan nan.
Tun daga lokacin ne ‘yan bindigar suka sha alwashin daukar fansa kan kisan da Akayi wa yi wa dan uwansu wanda suka dora laifin a kan mazauna unguwar.
A farmakin da suka kai wa al’umma a ranar Laraba, ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutum guda tare da neman N7m amatsayin kudin fansa nan take.
Wani mazaunin garin ya ce, “Ba mu ne muka kashe dan uwansu ba.
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya kara da cewa, ‘yan bindigar na farmakar garin na Magazu duk da cewa akwai jami’an tsaro a cikin al’umma.
Babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan jihar kan lamarin