Daga: Uzairu Lawal Rigasa
Wasu ’yan bindiga, a ranar Lahadin da ta gabata, sun kai farmaki wani otal mai suna 16 HOUR Hotel da ke unguwar Alomilaya na garin Ganmo, ta hanyar Ilorin a Jihar Kwara, inda suka kashe mai Otel din Mai shekaru 45 mai suna Kayode Akinyemi.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi a Ilorin a ranar Litinin, manajan otal din mai suna Emmanuel Olushila Ojo ya samu munanan raunuka a yayin harin da ake kyautata zaton kisan gilla ne, kuma a yanzu haka yana karbar magani a babban asibitin Ilorin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kenya: Madigun ‘Yan Adawa Odinga Ya Kalubalanci Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Kotu
Kakakin ya ce an yi garkuwa da daya daga cikin abokan mamallakin otal din, wani mai suna Ori da ke tare da shi a lokacin da lamarin ya faru.
Tawagar rundunar tare da ’yan banga da mafarauta sun bazama a cikin daji domin yiyuwar kubutar da wanda abin ya shafa tare da kama ’yan bindigar.
Ya kara da cewa, an ajiye gawar wanda aka kashe a babban dakin ajiyar gawa na asibitin yankin domin a duba gawarwakin.
Ana shi bangaren Kwamishinan ‘yan sandan jihar Talata Assayomo ya ayyana dokar hana fita baki daya a yankin, da kuma farautar wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Ya kuma sha alwashin cewa za a kama masu aikata laifukan tare da hukunta su, domin tuni an fara daukar tsauraran matakan tsaro domin dakile ayyukan masu aikata laifuka a fadin jihar baki daya.
A wani labarin kuma Zargin Ta’addanci: ‘Yan sandan Pakistan Na Tuhumar Tsohon Faraministan Kasar
Yan sanda a kasar Pakistan na tuhumar tsohon Firaministan kasar Imran Khan, da akaita laifukkan dake da nasaba da ta addanci.
Binciken nasu na zuwa ne bayan ya zargi yan sanda da ɓangaren Shari’a a kasar da tsarewa tare da azabtar da makusantansa, Kamar yadda BBC ta ruwaito.