• Rundunar yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da mutuwar matar.
•Matar ta mutu tana da shekara 66 ne da haihuwa kafin kisan.
• “Za a bayyana abun da bincike ya nuna nan bada jima wa ba”, Inji jami’in Hulda da jama’ a na rundunar yan sandan jihar.
A yau juma’a ce dai Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito cewa, wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun bi Uwargida Odetomi har gidan ta, da ke Ashi Bodija a garin Badun, sun harbe ta har lahira .
Jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, DSP Adewale Osifeso ne ya tabbatar da afkuwar lamarin, a cikin wasikar wayar hannu da ya aike wa NAN a garin Badun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar DSS ba ta Gayyace ni ba_cewar Gumi
Osifeso ya ce, “Kafin harbe Margayiyar, ta na da shekara 66 ne haihuwa” inji shi.
Inda ya Kara da cewa, “Nan ba da jimawa ba za a bayyana abun da bincike ya nuna kan lamarin.” Inji shi.