Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da muta ne sun kai farmaki kauyen Buwade da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto inda aka ce sun kashe mutane 11.
Wani tsohon shugaban karamar hukumar, Abdullahi Haruna Illela, wanda ya tabbatar da harin, ya ce ‘yan bindiga sun kuma yi awon gaba da mutane da dama a kauyukan Buwade da Dambo.
A cewar Haruna, ‘yan bindigan sun kai farmaki garin Buwade ne da misalin karfe 8 na daren ranar Talata “bayan Sallar Isha’i ba da dadewa ba kuma suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
“An tabbatar da mutuwar mutane 11 yayin da wasu da dama suka jikkata. Kauyukan biyu da ake makwaftaka da juna duk ba kowa.”
“Wasu daga cikin mazauna garin sun gudu zuwa garin Illela, yayin da wasu kuma suka gudu zuwa Gwadabawa inda da wasu ke Sokoto,” in ji shi.
Sai dai tsohon shugaban ya ce bai san da harin da aka kai a kasuwar Illela ba.
“Ban jin wani abu makamancin haka ba, amma na san sun yi awon gaba da dabbobi daga kauyukan biyu da suka kai hari,” in ji shi.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, ya yi alkawarin cewa zai sake kiran wakilin Majiyar jaridar Dimokuradiyya kan lamarin amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai tuntuba ba.