By Ishaq Dabai
‘Yan bindiga sun mamaye kauyen Saka-jiki a karamar hukumar Kaura-Namoda ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutane 12 tare da kona gidaje da shaguna da dama tare da Motoci da dama, ciki har da motar sintiri mallakar wani jami’in tsaro, maharan sun kone su.
Wani mazaunin kauyen,mai suna Malam Mohammed, wanda ya tsere zuwa garin Gusau, babban birnin jihar, ya shaida wa manema labarai cewa barayin sun mamaye kauyen a daren Alhamis data gabata inda suka kai harin.Mohammed yace duk da ba a yi garkuwa da kowa ba, amma ‘yan fashin sun kwashi kayayyakin abinci a kauyen.
“Ba su yi garkuwa da kowa daga ƙauyen ba amma sun tafi da kayan abincin mu da sauran muhimman abubuwan mu. Sun kuma kona gidaje da shaguna da ababen hawa da yawa kafin daga bisani su gudu zuwa maboyarsu, ”inji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace,“lamarin daya fi muni idan ba don jami’an tsaro su gaggauta shiga cikin lamarin ba. ”