By Abbas Yakubu Yaura
Wannan rana ce ta bakin ciki ga mazauna garin Kaduna biyo bayan wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a safiyar ranar Lahadi da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 a wurare daban-daban na jihar. Masu laifin sun kuma yi awon gaba da mutane 46 a yayin gudanar da aikin.
Al’ummomin da aka kaiwa harin sun hada da Angwar Zalla Udawa a karamar hukumar Chikun inda aka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da mutane 18 ‘yan gida daya.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na safiyar Lahadi a lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki kauyen da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
Wani shugaban al’ummar Udawa, Muhammed Umaru, wanda ya tabbatar wa manema labarai ya bayyana sunan marigayin da Bala Jaja.
Ya ce akwai matan aure da manya da kuma ‘yan mata daga cikin wadanda aka sace.
“Waɗannan mutane ne da na sani domin dukanmu muna zaune a wuri ɗaya. Bala Jaja wani matashi ne sananne a cikin al’umma kuma an kashe shi ne a lokacin da ya fito don taimakon makwabtan su da aka tafi da ‘yan uwa 18,” inji shi.
Hakazalika an kai wani hari makamancin haka a kauyen Kerawa da ke karamar hukumar Giwa inda aka yi garkuwa da al’ummar yankin 16 tare da kashe wasu biyar.
Wani tsohon kansila a yankin, Daiyabu Kerawa, wanda ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, ya ce garin ya zama ba kowa bayan harin.
A cewarsa, an yi jana’izar wadanda lamarin ya rutsa da su ne da misalin karfe 1 na rana Lahadi cikin fargaba.
’Yan bindigar sun kashe mutane biyar tare da sace wasu 16. Mun kammala jana’izar ne muna magana kan Babban abin bakin ciki shi ne babu wasu jami’an tsaro da suka kawo mana dauki a lokacin harin duk da an sanar da su,” inji shi.
Wani mazaunin yankin mai suna Jamilu ya ce mata da manya da kananan yara duk sun bar kauyen ne saboda tsoron kada ‘yan bindiga su kai musu hari.
“Bisa ga dukkan alamu ‘yan bindigar sun yi nasarar kauracewa kauyen mu saboda mutanenmu suna gudu da yawa. Wannan saboda ba mu da ‘yan sanda ko sojoji da za su kare kauyen,” inji shi.
Harin na uku ya faru ne a wata al’umma da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya mai suna Sabon Gida a karkashin Unguwar Tsalha Maraban Jos, karamar hukumar Igabi inda aka kashe wata matar aure tare da sace mutane 12.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce matar ta yi kokarin tserewa ne lokacin da ta ga ‘yan bindigar. Amma sun harbe ta har lahira.
Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar lamarin a hanyar Kerawa da Ungwan Rimi-Afana dake yankin Igabi da Zangon Kataf a wata sanarwa da ya fitar jiya.
A wani lamari makamancin haka, wasu ‘yan bindiga sun kashe wani manomi mai suna Irimiya Musa da wasu mutane biyar a kauyen Jauro Manu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘yan bindigar da adadinsu ya kai biyar, sun kai farmaki gidan babban manomin ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Asabar.
‘Yan bindigar, kowanne a kan babur, sun harbe shi a kofar gidansa kafin su harbe wasu biyar din da ke buga katin caca a wuri guda.
An kuma tattaro cewa Musa da wasu mutum hudu sun mutu nan take yayin da mutum na shida mai suna Haruna ya rasu a cibiyar kula da lafiya ta tarayya inda aka kai shi asibiti.
Wata majiya a kauyen ta shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai hari gidan manomin ne a ranar 10 ga watan Satumba, 2021 amma mutanen kauyen suka fatattaki ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Ya ce tun a wancan lokaci ba a kai hari kauyen ba har zuwa ranar Asabar din da ta gabata, inda ya ce an samu rudani a yankin saboda fargabar da ke tattare da mazauna kauyen.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce DPO na hedikwatar Mutum Biyu da ke karamar hukumar Gassol bai kai rahoto ga rundunar ba.