A kalla mutane 13 suka rasa rayukansu bayan da bindiga suka kai hari a kauyukan dake karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, kauyukan aun hada da Unguwar Gizo, Maigora, Sabon Layi da kuma Mai Ruwa.
Majiyarmu ta bayyana cewa ‘yan bidingar sun zo satar dabobbi cikin dare.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai cewa sun yi kokarin ganin sun hana ‘yan bindigar satar musu dabobbi.
“Maganar da nake ma a safiyar nan ta Juma’a zamu yi jana’izar mutane 13 da ‘yan bindigar suka kashe”. Ya bayyana.
“Wasu mutane bakwai sun samu raunuka kuma suna asibiti ana basu kulawa”.
Ya kara da cewa “akwai wani Mutum guda daya da suka harba a kaba a kauyen Mai Ruwa”.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-sanda-sun-cafke-matar-da-ta-saci-yarinya-yar-shekaru-2-da-haihuwa/
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin SP Gambo Isah yace “tabbas gaskiya an kashe mutane 13”.
“Mun sha jan kunnen mutane cewa da su guji tinkarar ‘yan bindigar saboda suna dauke da muggan bindigogi kirar AK-47, kuma babu yadda za a yi mutane su iya tunkararsu da bindigogin farauta”.
“Sun zo satar dabobbi ne su kuma mutanen kauyukan suka tasarmu wanda yasa ‘yan bindigar suka bude musu wuta”.