Akalla mutane 15 ne aka kashe a hare-haren da aka kai wa wasu al’ummomi a jihar Sokoto.
An kuma sace wasu mata a hare-haren, wanda ya faru kwanan nan.
Da yake tsokaci kan hare-haren, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana Gornyo da Illela a matsayin wasu daga cikin al’ummomin da abin ya shafa.
Da yake gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2022 ga majalisar dokokin jihar a ranar Litinin, Tambuwal ya ce, “Bari in fara da jajantawa al’ummar kananan hukumomin Goronyo da Illela kan harin da ‘yan bindiga suka kai a daren jiya, inda suka kashe mutane 12 a Illela da mutum uku a Goronyo.”
A cewar gwamnan, kalubalen tsaro na kawo cikas ga kokarinsu na kawo ci gaban jihar ta Sokoto, inda ya tabbatar da cewa za su ci gaba da mai da hankali wajen samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyi a jihar.
Da yake zantawa da Jaridar Daily Trust, dan majalisa mai wakiltar mazabar Illela a majalisar dokokin jihar, Bello Isa Ambarura, ya ce wasu ‘yan bindiga sun kai wa wasu kauyuka uku hari a yankinsa.
“Lallai wannan bala’i ne. Lamarin yana bukatar Allah ya kawo mana Dauki, Mun koma ga addu’a,” inji shi
Al’ummomin da barayin suka kai wa hari a Illela sun hada da Runji, Kalmalo da Munwadata.
A cewar dan majalisar, ‘yan fashin sun kuma yi awon gaba da wasu da dama.
Shugaban karamar hukumar Goronyo, Alhaji Abdulwahab Goronyo, ya ce an kashe mutane uku a wani kauye mai suna Kojiyo da ke yankin.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mata uku a yankin.