Akalla mutanen kauye 20 ne aka kashe a lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyuka da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Kauyukan da aka kai harin sune Kauran Fawa, Marke da Riheya da ke yankin Idasu, na karamar hukumar Giwa.
Kwamishinan kula da cikin gida da harkokin tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
A cewarsa, an kuma kona gidaje, manyan motoci, da motoci, tare da lalata amfanin gona a gonaki daban-daban.
Aruwan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai wanda ya samu rahoton cikin bakin ciki ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya.
Comments 1