Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane aƙalla 20 a harin da suka kai a daren ranar Laraba a ƙaramar hukumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna.
Mutane da dama sun ɓace bayan harin na kauyukan Apyiashyim, Atak’mawai, Kibori, da kuma Kurmin Masara a Masarautar Atyap.
“An kashe mutum 13 yawancinsu mata da ƙananan yara”, inji wani mazaunin Atak’mawai wanda ya ce maharan sun shiga ƙauyen nasu da misalin 1.00 na dare.
Wani mazaunin Apiashyim, Jonathan Ishaya ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutum shida suka kuma ƙona kusan rabin gidajen ƙauyen.
Ya ce maharan sun far wa ƙauyen ne da misalin 11.00 na daren suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
https://dimokuradiyya.com.ng/mazauna-yankin-zangon-kataf-sun-farmaki-fulani-makiyaya/
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar sun kashe kusan 13 a Kurmin Masara inda suka kona gidaje da dama.
A ƙauyen Kibori kuwa, mutane shida ne suka mutu aka kuma kona gidaje 10.
Maharan sun kuma kashe mutane uku a Mawai Zango inda suka cinna wa gidaje bakwai wuta.
Harin na zuwa ne bayan a ranar Talata an kai wa wasu Fulani makiyaya hari a lokacin da suke kiwo a ƙauyen Goragam a ƙaramar hukumar ta Zangon Kataf.
Sai dai har ya zuwa yanzu hukumar ‘yan sandan jihar bata ce komai ba, kuma wakilinmu ya kasa samun kakakin hukumar domin jin ta bakinsa.