By Ishaq Dabai
‘Yan bindiga sun sake kai farmaki Sarkin Pawa, hedkwatar karamar hukumar Munyan ta jihar Neja, a ranar Talata, inda suka kashe akalla mutane talatin.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Kachiwe kuma ya bazu zuwa sauran ƙauyukan dake ci gaba da zama a yankin.An ce sun isa kauyen akan Babura cike da makamai sannan suka fara harbi ba zato ba tsammani don tsoratar da mutanen garin wanda a sanadiyyar haka aka kashe mutane da yawa.
Daga kauyen Kachiwe,rahotonni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai farmakin su cikin al’ummomin da ke ci gaba da zama inda aka kashe da yawa.
Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, wanda ya tabbatar da harin a tattaunawar wayar tarho a Minna bai bayar da ainihin adadin wadanda suka mutu sakamakon hare haren ba.
Ya kuma tabbatar da mutuwar mutane uku yayin harin da ‘yan bindiga suka kai Kagara, karamar hukumar Rafi ta jihar a ranar Litinin. ‘yan bindiga sun bude wuta kan wadanda abin ya shafa, Kodayake jami’an tsaro basu tabbatar da afkuwar lamarin ba a matsayin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Gabriel Uba bai dauki kiransa ba kuma bai amsa sakon da aka aike masa dashi ba a lokacin da muke hada wannan rahoton amma Davidson Malison, Sakataren Yada Labarai na Kasa,na kungiyar cigaban Irigwe IDA ya tabbatar da hare haren da hotuna masu zafi.
A cewarsa, “Makiyaya sun tabbatar da kashe mutane hudu a ranar Talata da misalin karfe 6:50 na yamma.Mutum uku dake kan babur an yi musu kwanton bauna a kan titin Twin Hill, Jebbu Miango, gundumar Miango na Rigwe Chiefdom, biyu sun mutu nan take kuma daya ya samu rauni a harbin bindiga akan hanyarsu daga Jebbu Miango zuwa yankin Miango lokacin da makiyayan suka yi musu kwanton bauna inda Babur din da suke kai ya kuma kone kurmus.
“Da yamma kuma, an kashe mutane biyu a gona a Nzhwerenvi, Jebbu Miango, wadanda abin ya shafa sun hadar da Bitrus Bulus mai shekaru 45, Yakubu Chohu mai shekaru 35, Jumma’a Gani Kyeri mai shekaru 33 da Kyeri Gani mai shekaru 19,Musa Wah, matashi mai shekaru 27 ya ji rauni kuma yana jinya a asibiti.”