By Abbas Yakubu Yaura
An sami tashin hankali a yankunan Umologho da Isinweke dake garin Obowo da kuma garin Ihitte na karamar hukumar Uboma dake jihar Imo a daren jiya Juma’a bayan wasu Yan bindiga sun afka yankunan, inda suka kashe akalla Mutane uku.
‘Yan bindigar da suka afkawa garin cikin motoci kusan uku sun kuma kona babura kasa da 10 tare da jikkata wasu da ba a bayyana adadinsu ba.
A Umulogho, ‘yan bindigar da har yanzu ba a tantance aikinsu ba, sun kashe mutane uku musamman a mahadar Nwokeisiama.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wadanda lamarin ya shafa dai maza biyu ne da mace daya wadanda ke kwance cikin jini har zuwa lokacin hada wannan rahoto.‘Yan bindigar sun kuma harbe su ba kakkautawa kafin su shiga cikin garin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mike Abattam, bai tabbatar da faruwar harin ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Comments 1