Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da mummunan hari a wani wajen daurin aure a unguwar Ndiya Ikot Ukah cikin karamar hukumar Nsit Udium na jahar Akwa Ibom, inda suka kashe mutum daya.
Jaridar Punch ta ruwaito yan bindigan sun kashe wannan mutumi mai suna Godwin Thomas a yayin da tsaka da bikin daure a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, bikin da hatta gwamnan jahar, Udom Emmanuel ya samu halarta.
Yan bindigan sun dira gidan bikin ne jim kadan bayan gwamnan jahar ya tashi ya tafi, a daidai wannan lokaci ne suka kashe Godwin. Sai dai gwamnan ya bayyana damuwarsa bisa kisan matashin, sa’annan ya umarci jami’an tsaro su tabbata sun gano masu hannu cikin kisan.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labarun jahar, Charles Udoh ya fitar, yace Gwamna Udom Emmanuel ya jajanta ma iyalan mamacin, kuma ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta cigaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’an jahar.