Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata motar bas da ke dauke da dalibai, malamai da sauran matafiya a kan titin Okigwe zuwa Uturu, ‘yan mitoci daga Jami’ar Jihar Abia.
An tabbatar da cewa an harbe direban motar bas din
Hakan ya zo ne kwanaki biyu bayan da aka yi garkuwa da dalibai bakwai na Jami’ar Jihar Abia a hanyar.
Gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu, ya bayyana lamarin a matsayin wani sake yin garkuwa da mutane na rashin hankali da kuma kashe wasu ‘yan kasa wadanda da ba su ji ba ba su gani ba.
Ya ce jihar ba za ta bar wani abu ba, zakuma tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya cikin gaggawa, yana mai tabbatar wa Al’umar jihar hakan.
A wani labari Kuma Makamancin wannan
Yan bindiga Sun Sako Malamar Kwalejin Kaduna, Sun Rike Diyarta
Yan bindiga a ranar Talata da daddare, sun saki Dr. Rahmatu Abarshi, tsohuwar shugabar Sashen horas da fasahar Injiniya da Lantarki, ta kwalejin kimiyya da Fasaha ta Tarayya wato Kaduna Polytechnic.
Sai dai ’yarta Ameerah da direbanta na nan tsare a hannun ‘yan fashin.
DAILY POST ta ruwaito a ranar 24 ga Afrilu, shekarar 2022, yadda wasu ‘yan bindiga suka sace malamar , diyarta da direbanta a lokacin da suke dawowa daga unguwar Mariri a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Ta je raba wa ‘yan gudun hijirar kayan sawa ne a wani bangare na shirinta na “Barkindo Rahama Initiative”, lokacin da ‘yan bindiga suka kai musu hari, inda daga bisani suka bukaci a biya su Naira miliyan 100.
Abdallah Isma’il Abdallah, shugaban sahshin gudanarwa na Barkindo Rahama Initiative, wanda Dr Abarshi ta kafa, ya tabbatar da sakin malamar a daren ranar Talata, sai dai bai bayyana adadin kudin da aka biya domin sakinta ba.
Ya ce bayan ta samu ‘yanci a yammacin ranar Talata, an kai ta wani asibiti da ba a bayyana ba domin a duba lafiyarta.
Kazalika ya Kuma kara da cewa, “har yanzu ‘yarta da direbanta su na hannunsu Yan bindigan.”