A cikin wannan makon ce, wasu ‘yan bindiga su ka kashe mutum biyu a cikin gidajensu, a wasu hare-hare daban-daban wanda su ka kai a kamanan hukumomin Obio da kuma Akpor ta Jihar Ribas. Yayin da su ka kashe Anele Nwozuruaka, a yankin Alakahia da misalin karfe biyu na dare, inda su ka kashe Anebo Amadi da misalin karfe biyar na asuba a yankin Rumuekini. An bayyana cewa, sai dai yaran Nwozuruaka su ke ta rokon ‘yan bindigar a kan kar su kashe mu su mahaifinsu, amma ‘yan bindigar su ka ki jin rokon, inda su ka harbe shi har lahira.
Wata majiya ta bayyana cewa, maharani sun zo yankin Alakahia da yawa, inda su ka shiga gidan marigayi Nwozuruaka. Majiyar ta kara da cewa, wasu daga cikin maharani sun tsaya a waje, yayin da wadanda su ka harbe marigayin su ka shiga cikin gidan. Marigayi Nwozuruaka shi ne shugaban matasa na jam’iyyar PDP a yankin Alakahia.
Matar mamacin mai suna Misis Orlumati ta bayyana cewa, abin takaici ne mutuwar majinta, domin yaranta sun ta rokon maharani a kan kar su kashe ma su mahaifi. Da ta ke bayyana yadda lamarin ya faru, “mu na barci sai mu ka ji hayaniya a bakin kofarmu. Sai na tashi tare da majina, inda su ka shige cikin ban-daki. “Nan ta ke maharani su ka balle kofa domin su na da yawa, su na shigowa sai su ka tambayi mijina katin cire kudinsa, inda ya bayyana mu su cewa ya na cikin mota. Mijina ya bukaci su bi shi zuwa mota, amma sai su ka ki yarda. “Sun ja shi zuwa falo. Yarana tare da ni mu na ta rokon su, mu na ce mu su kar su kashe shi. Amma sai su ka harbe shi har lahira a nan take. Kalma ta karshe da mijina ya furta ita ce, mamana na tafi.”
Yayin mamacin mai suna Jeffrey Omejuriowhor-Amadi ya bayyana cewa, an kashe masa dau’uwa ne saboda ya na yaki da rashin gaskiya, ya na rokon jami’an tsaro da su binciko wadanda su ka kasha Nwozuruaka. “Mun ta shi kawai mun ga gawar kanina akwance wanda bai yin rikici da kowa. Shi ba dan kungiyar asiri ba ne, shi ba mutum mai yi wa mata fyade ba ne, kuma shi ba dan ta’adda ba ne, mun yi matukar mamaki. Shi dai kawai ya na yaki da rashin gaskiya,” in ji Omejuriowhor-Amadi.
Lokacin da a ka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar dukkan lamarin guda biyu. Ya bayyana cewa, kwamishinan ‘yan sandar jihar, Mustapha Dauda ya bayar da umurnin gudanar da bincike nan take ba tare da bata lokaci ba, inda ya bukaci ‘yan sanda su farauci wadannan mahara tare da gurfanar da su gaban kuliya. “Ina mai tabbatar da cewa, an kashe shugaban matasa na jam’iyyar PDP tare da wani mutum takanin jiya da yau. Kuma lamarin ya faru ne a yankunan Alakahia da kuma Rumuekini. “An kaddamar da gudanar da binciken lamarin. Kwamishinan ‘yan sandar jihar ya kafa dokar tabaci a kan sai an go wadanda su ka aikata wannan mummunan lamari tare da gurfanar da su a gaban kuliya. A yanzu haka an samu zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa,” in ji Omoni.