Yan bindiga sun farmaki kauyikan Ajiya da Yaaore dake karamar hukumar Batsari na jihar Katsina, in da suka kashe mutum biyu, Kuma suka sace shanu guda 35
Wani Shaida ya bayyana wa Jaridar LEADERSHIP cewa, Maharan sun afka yankunan ne a ranar Lahadi, dauke da muggan makamai, inda suka kashe mutum biyu, suka Kuma raunata mutum uku da harbin bindiga.
Magaji garin Yasore Abdurazak Mamman ya tabbatar da kai harin, inda ya ce daya daga cikin wadanda aka kashe, sun kashe Shi ne a gonara shi, inda kuma suka kadan dabbobin shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Matawalle ya Maida wasu masu bashi shawara bakin aikin su
Ya Kuma yi kira ga gwamnati da ta yi kokarin Samar wa da yankin tsaro, domin manoma su Sami damar komawa gona, don kara farfado da tattalin arzikin kasar nan.