Masu garkuwa da mutane sun kashe wani mutum mai suna Ayuba, tare da yin garkuwa da wasu ‘yan uwasa shida a cikin wata gona da ke unguwar Lagbeta a karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, al’ummar Labgeta na kan hanyar Abuja zuwa Lokoja da ke yawan hada-hada.
Dan uwan wadanda abin ya shafa Ishaya Bulus, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Laraba da misalin karfe 10:12 na safe a lokacin da wadanda abin ya shafa ke yin girbin amfanin gona.
“Sun shagaltu da girbin amfanin gona, sai ga masu garkuwa da mutane sun fito kwatsam suka fara harbe-harbe bindiga.”
“A lokacin da suke kai wadanda abin ya shafa cikin dajin ne daya daga cikinsu ya yi yunkurin tserewa, sannan daya daga cikin masu garkuwar ya bude masa wuta,” inji shi.
Ya ce an ajiye gawarwan wanda ya mutu a dakin ajiyar gawa, duk da a cewarsa har yanzu ‘yan uwan ba su ji ta bakin masu garkuwa da mutanen ba.
Wani dan banga a karamar hukumar Kotonkafe, wanda ya so a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, duk da cewa ya ce ‘yan banga na zagaya dajin domin gano maboyar barayin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Williams Ovye Aya, bai amsa kiran wayarsa ba, sannan kuma bai amsa sakon wayar da aka aike masa ba.