Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ba sun Shugaban Jam’iyyar APC na karamar hukumar Batsari Abdulhamid Sani Duburawa.
Dan majalisar da yake wakiltar karamar hukumar Batsari a majalisar jihar Hon. Jabiru Yauyau, shi ne ya bayyanawa jaridar THIS DAY, ta wayar tarho.
Ya bayyana cewa ‘yan bidingar sun je gidan mamacin dake Sabon-Garin Duburawa a kauyen Ruma da misalin karfe 12:47 a yau Lahadi. https://dimokuradiyya.com.ng/an-sake-kama-wani-dan-sanda-da-yayi-sanadiyyar-mutuwar-abokin-aikinsa/
Yace “gaskiya ne wasu ‘yan bindiga akan babura sun je gidan Abdulhamid Sani Duburawa, inda suka masa harbi da yawa sannan suka tsere”.
“An yu gaggawar kaisa babban Asibitin Batsari amma rai yayi halinsa, an dawo da shi gida domin yi masa sutura kamar yadda addini ya tanadar”.
Sai dai har yanzu kakakin hukumar’yan sandan jihar SP Gambo Isah, ba a samu ganawa da shi domin sake samun wasu bayanai.