Rahotanni da ke fitowa na nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani sufeton ‘yan sanda mai suna Idris Musa a unguwar Makera da ke yankin Kwakware na kan titin Katsina zuwa Jibia. Kamar yadda Channels TV ta ruwiato.
Wani ganau da aka (an sakaya sunansa) ya shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun isa unguwar ne a ranar Litinin da misalin karfe 7:00 na safe suna harbe-harbe a lokacin da suke bin wata motar safa da ke dauke da wasu fasinjoji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan ta’adda Sun Sace Matar Aure, Da Yar’ta A Jihar Neja
A cewar majiyar, kokarin da Sifeton ‘yan sandan ya yi na fatattakar ‘yan ta’addan ya ci tura, ko da suka mayar da wuta kan ‘yan sandan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’in.
Bayan harbe shi har lahira, an ce barayin sun kona motar Sufeto bayan sun yi awon gaba da fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba.
Har yanzu dai hukumomin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, amma da samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, ya ce yana wurin wani taron tattaunawa kuma zai yi jawabi ga manema labarai cikin nan da wani lokaci.
A WANI LABARIN KUMA: Tsohon Daraktan Hukumar NIMASA Ya Rasu A Landan
Tsohon Babban Daraktan Ayyuka na Hukumar Kula da Tsaron madatsun Ruwa ta Najeriya (NIMASA), Engr. Rotimi Fashakin ya rasu ne a lokacin da yake karatun lauya a kasar Ingila.
Tsohon jigon a jam’iyyar APC ya kasance kakakin rusasshiyar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC).