Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wani makiyayi suka kuma yi awon gaba da shanunsa a jihar Filato.
Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta ce an kashe makiyayin mai suna Jabiru Halilu ne a ƙauyen K/Vom da ke ƙaramar hukumar Jos ta kudu a ranar Juma’a.
Sakataren ƙungiyar a ƙaramar hukumar Riyom ta Jihar Filato ya ce an harbi Jabiru a kai ne a lokacin da yake kiwon dabbobinsa aka kuma sace dabbobin.
Ya ce daga baya ne jami’ai daga bbban ofishin ’yan sanda na K/Vom suka tsinci gawar mamacin.
Ya zuwa yanzu kakakin ’yan sandan jihar Filato, DSP Ubah Gabriel bai ce komai game da faruwa lamarin ba.