• Bayan ya cire makudan kudade ne a banki yan bindigan suka harbe shi har lahira a yau litinin
• Lamarin ya faru ne kusa da jami’ar Badun da kuma haryar Ojoo.
• “Rundunar yan sandan jihar Oyo ba ta tabbatar da afkuwar lamarin ba” A cewar NAN.
A na zargin wani da ba a san ko wanene ba ya mutu a yau litinin, kusa da madakatar motoci na Water dake kusa da jami’ar Badun zuwa hanyar Ojoo, bayan ya cire kudi a injin cire kudi na zamani wato ATM.
Kamfanin dillancin labaran kasar NAN ya ruwaito cewa, an harbi mutumin ne a Mafitsaran shi, inda a kayi gaggawar kai shi wani asibiti dake yankin Ojoo na garin Badun.
Kuma a nan ne aka tabbatar da mutuwar shi, inji NAN.
Wani shaidar gani da Ido, ya bayyana wa NAN cewa, an harbi mutumin ne, bayan ya cire makudan kudaden daga wani sabon banki, dake cikin jami’ar Badun.
Ya kara da cewa, a na zatun wadanda suka kashe shin, sun biyo shi ne har madakar motocin, inda a nan ne suka harbe shi, inji shaidar gani da idon.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hare haren Ebonyi: rundunar yan sandan ta baje kulin mutun 60 da ta ke zargi
Ya ce, “Naganshi lokacin da aka dauke shi zuwa asibiti a mota kirar Micra, lokacin na ta shi daga makaranta kenan, lamarin ya afku” inji shi
Sai dai ko da kamfanin dillancin labaran kasar Nan wato NAN ya tuntuni jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Oyo, DSP Adewale Osifeso, ya ce, haryanzu bai sami tabbacin faruwar lamarin ba.
Comments 1