By Abbas Yakubu Yaura
Akalla manoma 15 ne rahotanni suka bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai musu hari a kauyen Gakurdi da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina a ranar Talata.
Wannan ci gaban ya zo ne sa’o’i bayan da mayakan Boko Haram suka kashe manoma sama da 40 a jihar Borno.
Wani mazaunin garin ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa an kashe wadanda harin Katsina ya rutsa da su ne a lokacin da suke gyara gonakinsu gabanin saukar damina.
Ya ce ‘yan bindigar da suka hau kan babura hudu, sun nufi kauyen Gakurdi ne tun farko. Ya ce da suka ga manoman sai suka fara harbin su.
“Sun zo ne da misalin karfe 8:30 na safiyar yau (Talata), inda suka yi amfani da babura hudu suka fara kashe mutanen. An kashe uku a gona guda kuma daga karshe aka gano an kashe mutane kusan 15 a gonaki daban-daban,” inji shi.
Ya kara da cewa a lokacin da mutanen kauyen suka gano abin da ke faruwa, maharan sun gudu daga yankin.
A wani labarin kuma, ‘yan bindiga sun yi awon gaba da shanu sama da 100 a kauyen Danye Gaba da ke unguwar Bugaje a karamar hukumar Jibia.
An ce kauyen Danne Gaba yana da tazarar kilomita biyu da barikin sojoji na 17 dake Katsina.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce barayin sun tafi da shanun wadanda kusan mutane bakwai ne da misalin karfe 1:30 na safiyar ranar Talata.
Ya yi zargin cewa tun da misalin karfe 8 na daren ranar Litinin aka san motsin ‘yan ta’addan kuma an sanar da jami’an tsaro daban-daban amma ba a dauki wani mataki ba har sai da ‘yan bindigar suka kai hari.
Sai dai wani mazaunin garin da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an yi musayar wuta tsakanin masu laifin da jami’an tsaro a yayin harin.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, domin jin ta bakinsa, ya ce, “A yanzu haka muna nan tare da CP domin jin halin da ake ciki.