Wasu yan bindiga sun kai hari kan shingen binciken jami’an yan sanda a jihar Enugu, inda suka kashe yan sanda biyu nan take.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a wani shingen binciken yan sanda dake Nachi, na karamar hukumar Oji River a jihar Enugu.
Rahotanni sun bayyana cewa, yan sandan biyu sun mutu nan take sanadiyar harin yan bindigan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe ne ya tabbatar wa manema labarai Kai harin, inda ya ce, rundunar ta fara bincike domin ganin wadanda suka kashe yan sandan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim ya rasu
“An fara gudanar da cikakken bincike, wanda zai kai ga kamo maharan. Kuma za’ayi Karin bayani Dazaran ankama su ”in ji shi.
Wannan na zo wa ne, makonni kadan bayan makamancin irin wannan lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an yan sanda hudu, a yankin Amaechi Awkunanaw dake jihar Enugu.
A wani labarin cigaban Kuma.
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce jihohi bakwai na Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya sun amince za su dauki ‘yan banga 3,000 na musamman don taimakawa wajen yaki da’ yan fashi da mash garkuwa da mutane.
Masari ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da tambayoyi ga manema labarai a gefen Taron Tattaunawa da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed da sarakunan gargajiya, a Katsina ranar Talata. Sannan ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya ce za ta horas da’ yan bangar da za’a dauka.
A cewarsa, gwamnonin jihohin Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Kaduna, Neja, Katsina da Nasarawa sun gana kuma sun amince da daukar ma’aikatan da za su taimaka wa hukumomin tsaro wajen magance matsalolin tsaro a jihohin su.“Ba don kaina nake magana ba, amma a madadin gwamnonin jihohin da aka ambata a abaya.
“Batun ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da sassan Arewa ta Tsakiya ya rikide zuwa tawaye saboda haka mun kirkiro dabaru daban -daban don yakar barazanar da muke fuskanta, Akwai gungun’ yan bindiga sama da 150 a cikin dazuzzukan da suka yi mubaya’a ga shugabanninsu daban daban.
A nasa jawabin, ministan ya ce yana Katsina tare da manema labarai daga kungiyoyin kafafen yada labarai 22 domin samun bayanai na farko kan batun fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu da sauran su.
Mohammeed ya ce za a gabatar da cikakkun bayanan abubuwan da suka gano ga Shugaba Muhammadu Buhari don daukar matakin da ya dace.
Comments 1