An samu rudani a yankin Mahuta dake karamar hukumar Igabi yayin da ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu malaman jami’a biyu yan uwan juna, Malaman jami’ar, sun hada Dakta Adamu Chinoko da Dakta Umar Chinoko sai da suna aikin koyarwa ne a jami’o’i daban daban, shi dai Dakta Adamu Chinoko na koyarwa ne a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya yayin da dan uwa nasa Dakta Umar Chinoko ke koyarwa a makarantar kimiyya da fasaha na Kaduna (Kaduna Polytechnic).
Binciken da wakilinmu ya yi ya nuna cewa, da farko yan bindigar sun kama Dakta Adamu ranar Alhamis da daddare sai Dakta Umar ya tafi don kai musu kudin fansa na Naira Miliyan 2 da suka bukata kafin a saki dan uwan nasa a nan ne masu garkuwar suka kuma kama shi tare da yin garkuwa da shi jiya Lahadi.
Da yake tabbata da faruwar lamarin yayin da tawagar kungiyar al’ummar Zuru mazauna Kaduna suka kawo masa ziyara, Wakilin Sarkin Zuru a garin Kaduna, Injiniya Zubairu Kabiru Danjuma ya yi addu’ar Allah ya gaggauta kubutar da mutanen “Muna cikin bakin cikin garkuwa da su da aka yi saboda yan asalin jihar Kebbi ne akan haka muna addu’ar Allah ya kubutar da su, masu garkuwar sun bukaci Naira Miliyan 2 na fansar sai dan uwansa Dakta Umar da wani dan achaba suka tafi kai musu kudaden amma sai kuma suka kama su gaba daya,” inji shi.
Mai magana da yawun kungiyar yan asalin jihar Kebbi mazauna Kaduna, Garba Muhammad, ya bayyana cewa, masu garkuwar sun yi waya inda suke neman karin Naira Miliyan biyar kafin su sake su gaba daya. Ya kara da cewa, malaman biyu mutanen kirki ne a kan haka ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su gaggauta kubutar dasu tare da kawo karshen harkar garkuwa da mutane a kasar nan. Ya kuma ce tawagar kungiyar ta kai ziyarar jaje ga iyalan wadanda aka sacen. Kungiyar ta kuma yaba wa gwamnan jihar Kebbi a bisa kokarin da ya yi na ceto wasu ‘yan biyu da aka garkuwa da su a jihar kwanakin baya.
Da aka tuntube shi, jami’in watsa labarai na runudnar yan sandan jiha Kaduna DSP Yakubu Sabo, ya yi alkawarin sake kiran wakilinmu amma har aka hada wannan rahotn bai yi kiran ba.