Rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun tabbatar da kashe mutum guda tare da sace mutum uku a karamar hukumar Rafi a jihar. Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Abubakar Dan-Ina shi ne ya shaidawa jaridar Daily Trust hakan ta wayar salula. Inda ya ce lamarin ya auku ne a yayin da wadansu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Kusherki da misalin karfe 1 na dare a ranar Lahadi.
A cewarsa tuni rundunar ta musamman ta SARS suka bi sahu domin ganin sun kamo wadannan ‘yan bindigar, kuma za su tabbata da sun ‘yanto wadanda aka kama.
Zarnan Kusherki, Alhaji Garba Kusherki, ya ce; ‘yan bindigan sun zo ne a ababen hawa sama da 20, a yayin mutane ke bacci. Inda ya tabbatar da cewa; sun rika shiga gida-gida suna kai wa mutane hari suna neman kudi. Ya kara da cewa; sun fara da shiga gidan wani mutum mai suna Alhaji Abubakar Kaura inda suka nemi da ya ba su kudi, shi kuma ya ce ba shi da shi, sai kawai suka bude masa wuta, inda nan take bayan sun harbe shi a kai suka kashe shi. Sannan suka yi garkuwa da ‘yarsa mai suna Shamsiyya.
Ya kara da cewa; daga nan ne suka shiga gidan Alhaji Jafaru Jibrin Kusherki suka sace shi. Sannan suka sace dan uwan mai sarautar, mai suna Abdulrashid Mohammed. Ya tabbatar da cewa; ‘yan bindigar sun kwashe sama da awa guda suna wannan aika-aikar amma ba jami’in tsaron da ya kai musu dauki, duk da kuwa a cewarsa, akwai jami’an tsaro makarantar Sakandare ta gwamnati a kusa.
Har wala yau ya ce; sun tuntubi iyalan wadanda aka sace inda suka nemi da a ba su naira miliyan 20, amma ya ce ba wanda zai iya hada wannan kudin. Ya tabbatar da cewa; mutanen kauyen ba su taba fuskantar irin wannan al’amarin ba, duk da ana kai hare-hare a karamar hukumar ta su. Ya alakanta harin na su da ayyukan ‘yan bindiga dake aukuwa a jihohin makwabtansu wanda ya hada da Kaduna da Zamfara, ya ce musamman karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna da ta fi kusa da su.
Ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya akan a ba su tsaro a kuma tabbata a sanya jami’an tsaro a iyakar jiharsu da irin wadannan jihohi domin dakile kai irin wadannan hare-hare.