Majiyarmu ta shaidawa Dimokuradiyya cewa; ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai wa tawagar Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru hari a titin Abuja zuwa Kaduna inda suka yi awon gaba da shi.
Wani ganau ya shaida mana cewa lamarin ya faru ne da yammacin yau Talata kilomita kadan kafin a iso kwaryar cikin garin Kaduna.
Alhaji Hassan Attahiru Sarkin Gargajiya ne a jihar Zamfara.
Majiyarmu ta shaida mana cewa duk da Jami’an tsaron da ke raka tawagar Sarkin, hakan bai hana su sace Sarkin ba bayan da suka budewa tawagarsa wuta wanda hakan ya ba su nasarar tarwatsa tawagarsa.
Comments 1