Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewa wadansu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki kan garin Wara-Wara dake karamar hukumar Tsafe, inda suka yi awon gaba da tarin dabbobi kamar yadda rahoton gidan Rediyon Faransa ya labarto.
Majiyar da muka zanta da ita, ta shaida mana cewar, maharan sun afkawa garin na Wara – Wara ne da maraicen jiya asabar haye kan babura akalla 15, inda suka kore dabbobi akalla 500.
Majiyar ta ce ba a samu hasarar rai yayin harin ba, sai dai akalla mutane 9 sun jikkata, yayin da suke kokarin gudun tsira.
Jihar Zamfara dake arewa maso yammncin Najeriya na daga cikin jihohin da ke fama da hare haren ‘yan bindiga, barayin shanu da masu satar mutane don karbar kudin fansa.