Wasu yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba sun awun gaba da wata yar jarida dake aiki tashar watsa labarai na Jihar Adamawa wato Adamawa Broadcasting Corporation mai suna Amra Ahmad Diska.
Yat Jaridar wacce ke shayarwa, ba ta ma jima da dawowa daga hutun jego ba da aka bata ba.
Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar wadanda adadin su ya kai kimanin 15 sun kutsa ne gidan Yar Jaridar dake garin Mbamba na Karamar Hukumar Yola ta Kudu inda suka arce da ita.
Bisa rashin nasara da yan bindigar suka yi na mai gidan ta a gida, kawai sai suka wawure ta tate da jefar da jaririn ta mai kimanin watanni shida da haihuwa.
A yan baya-bayan nan dai lamarin yan bindiga na ci gaba da ta’azzara, musamman yadda suke addabar al’ummar ta Mbamba da kuma rukunin gidaje na Likitoci dake birnin Yola.