Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Farfesa Adamu Zata, masanin ilimin kimiyyar kasa na jami’ar kimiyya da fasaha ta Modibbo Adama dake Yola (MOUTECH), ranar litinin.
Haka kuma masu garkuwa da mutanen sun kuma kashe kanin Farfesan, Dakta Sheda Zata, wanda yake likitan babbobi a yunkurin sace Farfesan.
Majiyar iyalan Farfesan sun shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar da suka kai mutum 10, sun shiga gidan Farfesan dake karamar hukumar Girei, kimanin karfe biyun ranar Litinin, sun kuma kashe karamin Dan ‘uwanshi Dakta Sheda dan shekara 49.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ‘yan bindiga ke garkuwa da Farfesa Zata, domin kuwa ko cikin watan goman 2018, sun kame shi a gidan na shi dake kasa da mita 100 daga babban ofishin ‘yan sanda, da iyalansa suka tabbatar da cewa sun biya naira miliyan biyu kafin su sake shi.
Ita ma rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda DSP Suleiman Nguroje, shi ne kakakin rundunar ya ce tuni rundunar ta ba za jami’anta domin tabbatar da ganin an kai ga kame masu garkuwa da mutanen.
Yanzu haka mutanen da suka samu raunuka lokacin kai harin suna amsar magani a asibitin kwararru na gwamnatin jihar dake Yola.