Kaduna

‘Yan Bindiga Sun Saki Dalibai Mata 6 A Kaduna Bayan Biyan Miliyan 10

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar da suka sace dalibai mata guda shida a wata makarantar Sakandare dake Jihar Kaduna, sun sake su bayan sun karbi diyyar naira miliyan 10.

Jaridar Premium Times ta ce an saki daliban Makarantar ‘Engravers College’ ne yammacin Juma’a, inda daga bisani aka kai su ofishin ‘yan Sanda da kuma asibiti domin duba lafiyar su.

Arewacin Nijeriya ya kazanta da lamuran  garkuwa da jama’a a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da kokawa da rashin cikkaken tsaro a yankunan su.

Wasu daga cikin Iyayen yaran da suka ga ‘yayan su sun tabbatar da labarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *