Kwamishinan yada labarai na jihar Niger Mohammed Idris ya shaki iskar yan ci kwanaki kadan, bayan masu garkuwa mutane sun yi awan gaba dashi.
An saki Idris ne da misalin karfe 9:30 na daren jiya Alhamis a jihar Niger, Kuma nan take aka wuce da shi wata asibiti domin kula da lafiyar shi.
Rundunar yan sandan jihar ta Niger, ta tabbatar da sakin nashi a cikin wata sanar wa da tafitar, a safiyar yau juma’a.
Inda sanar war ta ce, “Shalkwatar rundunar Yan sandan jihar Niger, na sanar da daukacin al’umar cewa, Kwamishinan yada labarai na jihar Hon. Mohammed Sani Idris, ya shaki iskar yan ci daga hannun Yan bindiga batare da wani rauni ba”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cutar kwalara ta kashe mutum 146 a jihar Kebbi
Kazalika rundunar ta jaddada cewa, Yan bindigan sun sake shi ne batare da an biya ko si-si ba, a matsayin kudin fansa.
“Sakamakon matsi da tawagar hadakan Jami’an tsaro ke ci gaba da kai wa yan bindiga hare-hare, hakan ya sa masu Garkuwa da Kwamishinan, su ka sake shi a ranar 12 ga watan Ogustan shekarar 2021, da musalin karfe 09:30 na dare, inda su ka sake shi a yankin Kofa Dam na karamar hukumar Tafa, Kuma batare da bata lokaci ba, aka kai shi asibiti, domin duba lafiyar shi” inji sanar war.
Jaridar Dimokuradiyya dai ta ruwaito cewa, Yan bindigan sun yi garkuwa da Kwamishinan ne, lokacin da su ka afka karamar hukumar Tafa a kwanakin baya.