Mai Martaba Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu, ya shaki iskar Yanci daga hannun Yan bindiga.
Wani Shaida ne ya bayyana hakan inda iya ce, sauran mutum sha uku da Yan bindigan su kayi garkuwa da su tare da Sarkin a gidan shi, haryanzu su na tsare a hannun yan bindigan.
“An saki Sarkin Kajuru a wani daji dake kusa da yankin, da zai yi iso har garin Kajuru” inji Shaidan.
Wani daga cikin iyalan Sarkin ya bayyana cewa, Sarkin ya naxikin koshin lafiya Amma Tuni aka fara Shirin kai shi wani asibi dake garin, domin duba lafiyar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP ta yi babban kamu wani Dan jam’iyar APC
Kazalika Tsohon Shugaban Kungiyar Yan jaridu ta kasa dake Kaduna kuma mazaunin garin Ibrahim Inuwa Kajuru , ya tabbatar wa da Gidan Talbijin na Trust Tv sakin Basaraken, inda ya ce Sarkin ya yi Magana da Mabiya sa a fadar shi dake garin Kajuru” a cewar shi.
Sai dai haryanzu ba’a tabbatar, ko an bai wa yan bindigan kudin fansa ba, kafin sakin Sarkin, amma dai tun da fari, sun bukaci a ba su Naira milliyan dari biyu, kafin sakin Basaraken Mai shekara 85.