By Abbas Yakubu Yaura
Wasu dalibai mata hudu na Kwalejin Kimiyya da Fasahar kiwaon Lafiya da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da su kwanaki kadan da suka gabata a jihar Zamfara sun samu ‘yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
Mataimakin shugaban Kwalejin na Cibiyar, Jamilu Lawali ne ya tabbatar wa da Jaridar DAILY POST ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a daren ranar Alhamis.
DUBA WANNANLABARIN: Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Rukunin Gidaje 76 A Jihar Jigawa
A cewar sanarwar, wadanda suka yi garkuwa da su sun sako daliban mata hudu ne a ranar Alhamis a wani wuri da ke kusa da garin Tsafe.
Ya yi ikirarin cewa ba a biya kudin fansa ba a kafin a sako su.
“An sake su da yammacin yau a wani wuri kusa da garin Tsafe na jihar, makarantar ba ta biya kudin fansa ba,” in ji shi.
A cewarsa, daliban hudu a halin yanzu suna wani asibiti duk da bai bayyana cewa suna karbar magani ba.
Idan dai za a iya tunawa kimanin kwanaki biyu da suka gabata Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne, sun yi garkuwa da wasu dalibai mata 5 na Kwalejin Kimiyyar kiwon Lafiya ta Jihar Zamfara, amma daya ta tsere, hudu kuma aka garzaya da su zuwa inda ba a sani ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’an tsaro na kokarin ganin an sako su daga hannun ‘yan fashin.
Comments 1