By Ishaq Dabai
‘Yan bindiga sun sako daliban makarantar sakandare ta Baptist, da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta samu labarin cewa, an sako daliban tare da wani mutum a yammacin yau Juma’a.
Wata sanarwa dauke da sa hannun Rabaran Dr. Israel Adelani Akanji, Shugaban Babban Mabiya Darikar Baptist na Nigeria ya tabbatar da sakin Daliban.
Sanarwar ta ce, “Dalibai biyar na Makarantar Sakandare ta Betel Baptist da wani mutum an sake su a yammacin yau, 8 ga Oktoba.”
Indan za’a iya tunawa dai, Yan bindigan, a ranar 5 ga watan Yuli, sun mamaye makarantar tare da yin garkuwa da daliban makarantar 121, amma sun saki rukunin farko na dalibai 58 kafin wasu da suka biyo baya.