Dan takarar gwamna a shekarar 2019 a jam’iyyar AA da ke jihar Imo Uche Nwosu, ya shaki iskar ‘yanci. Idan dai za’a iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘’yan bindiga sun yi awon gaba da surukin tsohon gwamna Rochas Okorocha a coci ranar Lahadi.
Mai baiwa Nwosu shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Nwadike Chikezie, ya fada a ranar Litinin cewa ya tattauna da maigidansa wanda kuma ya mika gaisuwarsa ga wadanda suka tsaya tare da shi.
“Na yi magana da shi kuma ya mika gaisuwarsa ga dukkan mu dake wajen.
“Yayin da muke jiran rahoton ‘yan sanda kan dalilin daya sa aka yi garkuwa dashi da kuma kama su, muna kira ga kowa da kowa ya kwantar da hankalinsa kuma ya mai da hankali domin Allah ne ke kan lamarin baki daya.
“Aikin wulakanta dakin bauta da muka sani, cin zarafi ne da kuma fukantar jarrabawa ga Allah Ta’ala.inda ya kara da cewa “Mun bar Allah ya yi yaƙinsa domin fansa na Allah ne…”
Mai taimaka wa Sanata Okorocha kan harkokin yada labarai, Sam Onwuemeodo, ya shaida wa wakilinmu cewa Nwosu ya samu ‘yanci.inda yace “Eh an sake shi,” in ji shi.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo (PPRO), Michael Abattam, babban Sufeton ‘yan sanda (CSP), ya ce bai san ko an saki Nwosu ba.
“A hukumance, rundunar ‘yan sandan jihar Imo ba ta da masaniya kan sakin Uche Nwosu,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.