Manoman karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun amince su biya makudan kudade don ‘yan bindiga su barsu zuwa gonakinsu.
A cewar shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin-Gwari, Ishaq Usman Kasai, yan bindiga sun dorawa manoman haraji na miliyoyin naira.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, wannan na cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce manoman sun koma tattaunawa da ‘yan fashin ne saboda ba su da wani taimako.
Karanta kuma: Sabon Hari: Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 27 a jihar Kaduna
Ya ce an gurgunta ayyukan noma a Birnin-Gwari domin kusan kashi 70 cikin 100 na gonakin manoma ba sa iya samun damar yin amfani da su a cikin shekaru uku da suka wuce.
“A mafi yawancin al’ummomi, manoma sai sun biya miliyoyin Naira kafin a bar su su shiga gonakinsu.”
“Wasu yarjejeniyoyin da aka cimma a tattaunawar da bangarin suka yi da manoman sun hada da baiwa manoma damar shiga gonakinsu ba tare da yin garkuwa da su ba ko kuma wata hanya ta tsoratarwa da ‘yan fashin zasu yi, za a bar ‘yan fashin na zuwa garuruwa da kauyukan da ake zaman sulhu ana shigar da su don kiwon lafiya, saye da siyarwa da kuma duk wani kasuwanci na yau da kullun, ”in ji shi.
Ya kara da cewa tattaunawar ta baiwa manoman da ‘yan bindigar suka kora daga aiki a cikin al’ummomi irin su Katakaki, Ganda, Mashigi, Ginsa, Biskin, Layin Mai-Gwari, Kwasa-Kwasa da sauransu da dama damar su shiga gonakinsu.
BEPU ta kara da cewa ‘yan bindiga da dama suna da gonaki a wadannan Al’ummomin, inda ta kara da cewa fitaccen sarkin yakin, Dogo Kachalla Gide, yana da gonaki a yankin Mashigi.
Kasai ya ce ‘yan bindigar sun dakatar da sace-sacen mutane da kai hare-hare a wasu al’ummomi amma sun ci gaba da kwace babura da wasu kayayyaki masu daraja daga hannun manoma.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta dauki duk wani mataki da ta ga ya dace domin hana ‘yan ta’adda haddasa rashin zaman lafiya a Birnin-Gwari da kewaye.
Da aka tuntubi kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, bai amsa kiran waya ba ko kuma amsa sakon da aka aike, kamar yadda jaridar Daily trust ta bayyana.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce zai samu cikakken bayani daga rundunar ‘yan sandan yankin.
Ya kuma bukaci al’ummar yankin da su rika bayar da bayanai ga jami’an tsaro.
A wani labarin kuma: An Yi Garkuwa Da ‘yan Kasuwa 70 A Babbar Hanyar Birnin Gwari Zuwa Kaduna
Sama da ‘yan kasuwa 70 ne ake fargabar an yi garkuwa dasu a ranar Laraba a lokacin da wasu ‘yan bindiga da suka addabi yankin Birnin Gwari suka kai hari kan ayarin motocin ‘yan kasuwa a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.
A cewar wata majiya, ayarin motocin sama da 20 tare da rakiyar ‘yan sanda na jigilar ‘yan kasuwa ne daga kauyukan karamar hukumar Birnin Gwari zuwa Kaduna da Kano, inda ‘yan bindigar suka far musu.