A wadansu tagwayen hare-hare da wasu ‘yan bindiga suka kai akan yankin dajin Allawa da ke tsakanin kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar Neja, maharan sun fatattaki kauyuka 4 daga matsugunansu.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai maharan suka yi wa kauyen Kukoki da ke a karamar hukumar Shiroro dirar mikiya suka fatattaki mutanen kauyen, inda a jiya Laraba kuma suka sake kai irin wancan hari akan kauyika uku a karamar hukumar Rafi.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa, wani shaidar gani da ido ya bayyana mata cewa mahara dauke da bindigu sun hari kauyukan Rafin-Wayan, Rafin Kwakwa da Gidan Dogo-Gurgu a bisa babura guda ashirin da daya kuma sun yi goyon uku-uku akan kowane babur.
Maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi a dukkan kauyukan da suka kaiwa hari, inda mazauna kauyukan suka fece don gudun tsira da rayuwarsu, amma duk da haka maharan sun debi mata da yawa sun tafi da su.
Mazauna wadannan kauyuka dai sun samu mafaka ne a garin Kagara, inda nan ne fadar gwamnatin karamar hukumar Rafi ta ke. Kuma sun kafa sansani a gine-ginen gwamnati na ma’aikatu da ofis-ofis.
Malam Dahiru ya bayyana cewa, maharan sun yi musu kawanya ne a kauyen Rafin Wayam, inda suka saci kayan abinci da yawa kafin su fita daga kauyen su shiga kauye na gaba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Muhammad Dan Inna Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya shaidawa jaridar ta Leadership cewa bashi da takamaimai adadin mutanen da suka rasa rayukansu ko na wadanda suka jikkata a kauyuka hudun da aka kaiwa hari.
Ya kuma kara da cewa, rundunar tasu a yanzu haka na kokarin sauya fasalin tsaron kauyukan da abin ya shafa don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Haka kuma a wani rahoton, mahara sun kai hari kan kauyukan da ke iyaka da Birnin Gwari ta jihar Kaduna. Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a jiya Laraba ya yi wata tattaunawa ta tsawon sa’o’i da dama da hukumomin tsaro na jihar, inda aka tattauan yadda za a shawo kan rashin tsaron da ya ke neman ya addabi jihar.