Rahotannin da ke shigo mana na nuni da cewa; ‘yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon shugaban karamar hukumar Olamaboro da ke jihar Kogi, Mr Emmanuel Ekpa.
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP William Aya ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawarsa da manema labarai ranar Lahadi, inda ya ce, an sace Akpa ne akan hanyar Ochadamu da ke karamar hukumar Ofu.
Sai dai ya ce ‘yan sandan da ke aiki a yankin ne ne suka lura da mota yashe a ranar 18 ga watan Disamba kwana daya bayan da aka sace shi.
Sai dai ya tabbatar da cewa, tuni kwamishina ‘yan sandan jihar, Edeh Ayuba ya umarci dakarunsa su tabbatar da sun ceto shi daga hannun ‘yan ta’addan.